Amirka na bukatar a binciki Rasha
February 23, 2020Talla
Trump ya ambata hakan ne ga manema labaru a Fadar White House a lokacin da ya ke shirin kai ziyara kasar Indiya, inda ya ce ba a sanar da shi hakikanin abubuwan da bayanan suka kunsa ba, musamman a kan yakin neman zaben Mr. Sanders.
A gefe guda kuma shugaban na Amirka ya taya abokin hamayar sa murnan lashe zaben fidda gwani na jihar Nevada.
Ana dai zargin Rasha da yunkurin yada wasu labarai mara kan gado da ma wasu nauika na farfaganda a zaben na Amirka da ke tafe.