1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na rarrashin Saudiyya

Usman ShehuNovember 4, 2013

Ƙasar Amirka na yunƙurin kwantar da hankali babbar ƙawarsu a ƙasashen Larabawa wato Saudiyya, bayan da aka samu saɓani bisa yunƙurin Amirka na maida hulɗa da Iran

https://p.dw.com/p/1ABIf
U.S. Secretary of State John Kerry (L) is traditionally welcomed with coffee from Saudi Foreign Minister Prince Saud Al-Faisal bin Abdulaziz al-Saud November 3, 2013. REUTERS/Jason Reed (SAUDI ARABIA - Tags: POLITICS ROYALS)
Hoto: Reuters

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yana birnin Riyadh, inda ya ke ganawa da Sarki Abdullah na Saudiyya. Ana dai ganin wannan ziyar ta Kerry a matsayin ƙoƙarin kwatar da hankalin mahukuntan Saudiyya, waɗanda a yanzu suka ruɗe, sakamokon jin cewa Amirka za ta maida hulɗar difalmasiya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A gefe guda Saudiyya na nuna fushi kan yadda gwamnatin Amirka ta kasa yin wani abu bisa yadda ta gyale Isra'ila ke ci-gaba da gina gidaje a yankunan Falashinawa. Abu na uku da Saudiyya ba ta ji daɗin Amirka ba shi ne, yadda Amirka taƙi ɗaukar matakan da za iya kawar da gwamnatin Bashar Alssad, wanda Saudiyya ke jagorantar ƙasashen Larabawa don mai da shi saniyar ware da kuma ganin bayansa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamad Awal Balarabe