Sudan na bukatar gwamnatin farar hula
January 3, 2022Talla
Ofishin kula da al'amuran Afirka a ma'aikatar hakokin wajen Amirka a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter ya ce bayan murabus din firaminista Hamdok akwai bukatar shugabannin Sudan su kawar da banbance banbancen da ke tsakaninsu don samun masalaha yadda kasar za ta cigaba kan tafarkin dimukuradiyya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ya kamata firaministan Sudan na gaba da 'yan majalisarsa a zabo su bisa tafarkin kundin tsarin mulki domin cika burin al'ummar kasar na samun 'yanci da zaman lafiya da kuma wanzuwar adalci.
A ranar lahadi ne firaminista Hamdok ya yi murabus bayan tsawon makonni ana fama da zanga zangar adawa da gwamnati da rashin kwanciyar hankali da sojoji da ke jagorancin kasar.