Amirka ta ce Duniya ta amince da Guaido
April 10, 2019Talla
Mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ne e lokaci ya yi da Majalisar Dinkin Duniya za ta amince da jagoran adawar kasar Venezuela Juan Guaido, a matsayin halattacen shugaban kasa.
Mr Pence ya shaida wa kwamitin sulhu na majalisar ta duniya cewar fadar White House, za ta mika daftarin bukatar kafa Guaido a matsayin shugaban na Venezuela, tare da nada wakilin kasar a majalisar ta dinkin duniya.
Amirka dai na daga cikin kasashen duniya 50 da suka amince da Mr Guaido wanda tuni ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.
Ya kuma shawarci Mr Guaido, da ya hanzarta komawa birnin Carakas don isar da sako ga Shugaba Nicolas Maduro.
Sai dai a bayyane take kasar Rasha na iya hawa kujerar na ki.