1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce yaki da IS zai dau lokaci

Ahmed SalisuDecember 3, 2014

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce akwai yiwuwar daukar shekaru da dama kafin a kai ga cimma 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular musulunci a Iraki da Siriya.

https://p.dw.com/p/1DyhQ
Explosion in Kobane
Hoto: Getty Images

Kerry na wadanan kalamai ne dazu a birnin Brussels na kasar Belgiyum inda ya ke cewar gamayyar kasashen da Amirka ke jagoranta a yakin da IS na samun cigaba kuma za su cigaba da fafutuka ta ganin sun karya kashin bayan 'yan kungiyar duk kuwa da irin girman kalubalen da ke gabansu.

A hannu guda kuma sakataren na harkokin wajen Amirka ya ce a karon farko Iran da ta jima tana zaman doya da manja da Amirka ta kai farmakinta na farko kan 'yan kungiyar ta IS duk kuwa da cewar ba ta cikin gamayyar kasashen da yaki da su, to sai dai firaministan Iraki Haider al-Abadi ya ce basu da masaniya dangane da harin da Iran din ta kai.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Irakin ke cewar matar nan da aka bada labarin kamata a Lebanon wadda ak ce mai dakin shugaban kungiyar IS ce, ba ta cikin jerin matansa. Ma'aikatar cikin gidan Irakin da ta yi wadannan kalaman ta ce matar mai suna Saja kanwa ce ga wani mutum da ake fuskantar hukuncin kisa a Iraki sakamakon samunsa da laifi na aiyyukan ta'addanci.