Sudan ta fita cikin masu taimakon ta'addanci
December 14, 2020Talla
Matakin zai bude wa Sudan kofar samun agaji da sassaucin basussuka, tare da shigowar masu zuba jari domin farfado da tattalin arzikin kasar da ke fama da matsi, yayin da a gefe guda kasar ke fama da rikicin siyasa da annobar Corona.
Shekaru 27 kenan Amirka ta sanya kasar Sudan cikin jerin kasashen da ke tallafawa 'yan ta'dda, sai dai a watan Oktoban 2019 Shugaba Donald Trump ya yi alkwarin wanke sunan Sudan.