1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na jibge sojoji a kan iyakar Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
April 2, 2021

Wata sabuwar dambarwa na neman kunno kai tsakanin Rasha da Amirka bayan da Rasha ta fara jibge sojojinta a kan iyaka da kasar Ukraine, abin da Amirka ta ce tsokanar fada ce.

https://p.dw.com/p/3rWQB
Russische Militärfahrzeuge an der russisch-ukrainischen Grenze
Hoto: Reuters/Stringer

Amirka ta gargadi Rasha akan jibge sojoji a kan iyakarta da kasar Ukraine. Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ta damu matuka inda ta baiyana matakin na Rasha a matsayin tsokanar fada kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Amirka Ned Price ya shaidawa yan jarida.

A ranar Alhamis sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Andriy Taran game da batun.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Moscow da jibge sojoji a iyakar kasarsa daura da yankin Crimea da Rasha ta kwace domin tada fitina. Ukraine din dai ta dade tana takun saka da yan aware da ke samun goyon bayan Rasha tun shekarar 2014.

Wasu manazarta na ganin matakin Rasha na tura sojoji kan iyakar Ukraine a matsayin gwaji ga gwamnatin Amirka ta shugaba Joe Biden wanda a watan Maris da ya gabata ya janyo cece-kuce bayan da ya kira takwaransa na Rasha Vladimir Putin a matsayin makashi.