Amirka ta hana shiga daga nahiyar Turai
March 12, 2020Shugaba Donald Trump ya sanar da dakatar da dukkan wasu tafiye-tafiye daga kasashen Turai zuwa Amirka in banda kasar Birtaniya na tsawon kwanaki 30. A jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin daga White House, Shugaba Trump ya ce matakin zai fara aiki ne daga karfe 12 na daren ranar Jumma'a.
Ya ce irin matakin da aka dauka kan zirga-zirga tsakanin kasar da China da wasu kasashen a farkon bullar cutar, ya taimaka wajen rage yawan wadanda suka kamu da ita a Amirkar, idan aka kwatanta da yanda ta ke yanzu a Turai.
A halin da ake ciki dai kasar Italiya da ke nahiyar Turai, na fama da yaduwar cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta zama annoba gama duniya, da ya kai ga hana zirga-zirga a kasa baki daya. Kasashe 26 ne dai na Turan wannan mataki na Amirka ya shafa.