Amirka ta nemi izinin majalisun kasar kan IS
February 11, 2015Talla
A farkon fari dai lokacin da jiragen yakin kasar ta Amirka suka fara yakar 'yan kungiyar ta IS, 'yan majalisu da dama na Amirka sun soki lamirin matakin na shugaba Obama na yin gaban kansa ba tare da amincewar majalisar ba, inda suke ganin yana fuce gona da iri
A wannan takarda da ya aikewa majalisar Shugaba Obama ya takaita wa'adin izinin da yake nema ya zuwa shekaru uku, inda zai yi amfani da karfin gaske wajan yakar 'yan kungiyar. Majalisun biyu na Amirka dai zasu yi nazanin wannan takarada ta Shugaba Obama, inda ake sa ran tafka mahawara a kan ta tsakanin 'yan demokrate da 'yan Republicain wadanda suke kallon cewa Shugaban na nuna sassauci a kan batun yakar 'yan jihadin.