Shugabar kotun kolin Amirka ta rasu
September 19, 2020Talla
Ana yiwa maragianyiya Ruth Bader Ginsburg kallon cikakkiyar 'yar rajin kare doka da oda uwa uba da 'yancin mata a kasar, lamarin da ya kai shugaba Donanld Trump da jinjinawa rayuwarta yana mai bayyana cewa ta nuwa jan namijin kokari.
Tuni fadar White House da majalisar dokokin kasar suka bayyana sasauta tuta a wani mataki na jimamin rasuwar, kana kuma jama'a da dama na ci gaba da nuna alhinin rasuwar shugabar kotun inda suka yi dafifi a harabar kotun tare da kunna kyandura da ajiye furanni.
Mai shekaru 87 a duniya Ruth Bader Ginsburg ta rasu ne a yammacin jiya bayan tayi fama da rashin lafiya, to amma sai dai kuma mutuwar ta na zuwa ne a daidai lokacin da ake dab da gudanar da zaben kasar.