Amirka ta tura dakarunta Sadiyya
July 20, 2019Talla
Sarki Salman na Saudiyya ya ce matakin ya biyo bayan fahimtar juna tsakanin kasashen biyu domin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa tun kafin Iran ta fara takun saka da Birtaniya kan kwace jiragen dakon man Birtaniya Amirka ta aike da tawagar dakarunta zwua Saudiyya, amma ma'aikatar tsaro ta Pentagon ba ta tabbatar da matakin a hukumance ba sai a baya-bayannan. Tun a shekarar 2013 ne rabon Amirka da tura sojoji Saudiyya bayan janyewar dakarun loakcin da aka gama yakin yakin kasar Iraki.