Amirka ta sanya takunkumi kan masu taimakon IS
September 29, 2015Talla
Baitul malin kudaden Amirkan a yayin bayar da sanarwar tace takunkumin zai fara aiki ne ga jagoror goma 15 cikin su hadda masu goya musu baya da masu gudanar da kungiyar ta ISIS.
Sanarawar ta kara da cewar mutane goma da karin wasu kungiyoyi biyar masu ayyukan ta'addanci da suka hada da 'yan kasashen Faransa da Britaniya an sanaya musu takunkumin.
Bailtul malin Amukan yace irin yadda kungiyar ke cigaba da bazuwa ya zama wajibi a dauki kwararan matakai ta hanyar dakile irin hanyoyin da suke samin tallafin kudade a gurare da dama.