SiyasaAfirka
Amirka ta shawarci Sudan kan zaman lafiya
April 5, 2021Talla
A wata tattaunawa a tsakanin Firaiminista Abdallah Hamdok da Sakataren harkokin wajen Amirkan Antony Blinken, Blinken ya shawarci samar da damar shimfida tsare-tsaren inganta sauye-sauye a kasar da ta sha fama da zanga-zangar neman sauyi, bayan kifar da gwamnatin Oumar Hassan al-Bashir na sama da shekaru talatin.
Hakazalika sun tabo batun takaddamar kasar ta Sudan da Habasha kan shirin Habashan na gina madatsar ruwa a kan kogin Nilu, wanda tuni ake ganin barazana ce babba ga kasashen yankunan da ke zagaye da kogin. Suna dai fuskantar matsin lamba daga kasashen waje kan su cimma yarjejeniya guda mai ma'ana bayan kasa cimma matsaya a duk yunkurin baya.