Larabawa ba sa taimaka wa Falasdinawa inji Amirka
July 24, 2018Talla
Jakadar Amirka a majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta soki kasashen Larabawa da sauran kasashen musulmi da yawan babatu akan nuna goyon bayan Falasdinawa amma kuma basa bada gudunmawar kudi domin tallafa musu inda ta ambaci kasashe kamar Masar da Kuwait da kasar hadaddiyar daular larabawa.
Harley ta kuma nuna yadda kasashe irinsu Algeria da Tunisia da Pakista da Oman da kuma Turkiyya walau dai basu bayar da komai ba ko kuma abin da suka bayar din bai taka kara ya karya ba wajen taimaka wa hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniyar da ke agazawa Falasdinawa 'yan gudun hijira.
Amirka wadda ita ce ta fi bada tallafin jin kai ga hukumar jin kai ta rage dala miliyan 60 daga cikin alkawarin da ta yi na dala miliyan 365 a bana.