Amirka ta soki kawayenta
April 28, 2018Sabon sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo, ya soki kawayen Amirka musamman kasar Jamus da rashin himmatuwa ga batun samar da kudade wa kungiyar tsaro ta NATO. Sakataren harkokin wajen na Amirka, wanda ke magana a ganawar da suka yi da kawayen Amirkar a Brussels na kasar Beljiyam, ya ce Jamus na matukar jan kafa, wajen samar da isassu yadda kungiyar ke so.
Sai dai fa ministan harkokin wajen Jamus Heiko Mass, ya shaida wa babban jami'in diflomasiyyar Amirkar irin kudaden tallafin da kasarsa ke kashewa a kasashen Syria da kuma Iraki. Mr. Mass ya kuma ce sabuwar gwamnatin Jamus na shirin samar da sabon kasafi ne na kudi, ba kuma tare da ya fito kai tsaye ya yi alkawarin kara wa kungiyar tsaron ta NATO kudaden da take bukata ba.
Shugaban Amirka Donald Trump dai ya sha caccakar kawayen kasarsa da gaza samar da kudaden, wadanda suke matsayin kashi biyu cikin dari na kudaden da kasashen ke samu daga kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida, don gudanar da harkokin tsaron kungiyar.