Amirka ta tura jiragen yaki a Iraki
August 8, 2016Talla
Cibiyar tsaron kasar Iraki ta karbi bakoncin sabon rukunin jiragen yaki na kasar Amirka, wannan dai na zama wani yunkuri na hadin gwiwar kasashen biyu na yunkurin murkushe mayakan IS ake fafatawa da su shekaru biyu.
Dama dai jiragen yaki 36 ne Amirka za ta sayar wa Bagadaza amma kawo yanzu jiragen samfarin F16 guda takwas ne suka isa kasar. A tun shekara ta 2014 kasar Iraki ke fuskantar barazana daga mayakan IS amma a bara dakarun gwamnati da na hadin gwiwar Amirka na samun nasarar kwace manyan birane da mayakan na IS ke iko da su.