An nemi Saudiyya ta baiyana dan jaridan da ya yi batan dabo
October 11, 2018Talla
Gwamnatin Trump na da nan da watannin hudu na bayar da sakamako kan binciken dan jaridan da ke da takardar shedar zaman kasar. Akwai yi yuwar Amirka ta azawa kasar Saudiyya takunkumi muddun aka gagara gano inda Kashoggi ya yi.
Saudiyya na ci gaba da fuskantar matsi daga bangarori daban-daban kan batan dabon da Kashoggi ya yi a ranar biyu ga wannan watan na Oktoba. An dai yi wa dan jaridan gani na karshe a ranar da ya shiga ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Kasshogi ya yi kaurin suna a son sukar gwamnatocin kasashen Larabawa da kuma wasu manufofin kasarsa ta asali wato Saudiyya.