Amirka tana nan kan manufofinta
January 31, 2018Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi kiran hadin kan Amirkawa tare da tabbatar da tsare martaba gami da iyakokin kasar, a jawabin farko da ya yi wa zaman hadin gwiwa na majalisun kasar ta Amirka bayan gwamnatinsa ta cika shekara guda kan madafun iko.
Jawabin na Mr. Trump wanda ya fi mayar da hankali kan matsalolin cikin gida, ya kuma maida hankali ga tsaurara matsayi kan shige-da-ficen baki.
Shugaban na Amirka ya kuma tabbatar da matsayin Amirka kan janye tallafin da take bai wa kasashe da ya bayyana da makiyan Amirkar, bayan nuna adawa da matsayin birnin Kudus bisa zama fadar gwamnatin Isra'ila.
Haka nan Mr. Donald Trump ya gargadi mahukuntan Koriya ta Arewa, wadanda ya ce la-budda, take-takensu babbar barazana ce ga kasar.
Ya kuma jaddada cewar za a ci gaba da barin sansanin gwale-gwale na Gwantanamo a bude, saboda duk wani makiyi na Amirka.