1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump zai fice daga jam'iyyar Republican bayan ya sauka

January 20, 2021

Shugaba Donald Trump da ke sallama da mulkin Amirka a wannan Laraba ya nuna alamun kafa sabuwar jam'iyya ta kishin kasa amma ta kashin kansa.

https://p.dw.com/p/3oAo7
Symbolbild USA Trump Abschied
Hoto: Carlos Barria/REUTERS

Mujallar Wall Street Journal ta ce tun a makon da ya gabata Mr. Trump ya fara tattaunawa da makusantansa domin ganin sun kafa jam'iyyar da suke son sanya mata suna "Patriot Party" da babbar manufar sanya Amirka a gaban duk abin da jam'yiyyar za ta yi, kamar yadda trump din ya sha ikirari.

Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan jam'iyyar Trump ta Republican sun fito karara sun yi alla-wadai da dabi'un da shugaban mai barin gado ya nuna a kwanakin karshe na mulkinsa. Sai dai kuma masu sharhi na cewa da wahala idan har jam'iyyar da Trump din zai kafa ta iya kai labari, ganin cewa manyan jam'iyyun Amirka na ci gaba da nesanta kansu daga manufofinsa.