Donald Trump ya ce za su kori bakin haure
June 18, 2019Talla
Shugaba Donald Trump wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ya ce akwai miliyoyin mutane da ke zaune a Amirka wadanda suka shiga kasar ba cikin kai'da ba, wadanda ya ce za su mayar da su kasashensu da gaggawa daga duk inda suka zo. Tun farko Amirka ta gargadi kasashen Amirka ta tsakiya da cewar za tai daina ba su tallafin kudade inda har ba su dau matakan dakatar da tudadar 'yan gudun hijira ba.