SiyasaGabas ta Tsakiya
Za a kai Saudiyya kotu bisa harbe-harben da sojinta ya yi
February 23, 2021Talla
Takardun shigar da karar da aka rubuta a ranar Litinin sun yi zargin cewa Saudiyya na da masaniya cewa Alshamrani soja ne mai tsastsauran ra'ayi kuma ya na da alaka da kungiyar al-Qaida amma duk da haka Saudiyyar ta tura mata shi a cikin sojojinta da suka je barikin sojin ruwa na Florida domin yin wani kwas na soja.
Bude wutar da sojan na Saudiyya dai ya yi a ranar 06.12.2019 ta kai ga mutuwar sojojin Amirka uku da suka mutu bayan da ya bindige su.