Amirka za ta sallami sojojin Saudiyya
January 12, 2020Talla
Duk da cewa matakin na da alaka da zargin tsauraran akidu, ana kuma zargin sauran sojoji 11 da zargin cin zarafin kananan yara da hoton batsa da hukumar bincike ta FBI ta bankado tare da taimakon kamfanin apple.
Har lokacin wallafa labarin Saudiyya ba ta ce komai kan matakin korar sojojinta da ke makarantar horon soji a Amirka ba, amma akwai sojojinta 850 da ke makarantar horon da wasu sojoji 5000 na kasa da kasa.