Najeriya: Yiwuwar hana shiga Amirka
January 22, 2020Talla
Shugaba Donald Trump ya bayyana aniyar tasa ne yayin da yake jawabi a zauren babban taron tattalin arziki na duniya a birnin Davos na kasar Switzerland. Mujallar Wall Street Journal ta Amirkan ta ruwaito cewa, hanin zai shafi kasashe bakwai da suka hadar da Najeriya da ke zaman kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da kuma wasu kasashen na AFirka da Asiya, kana su ma kasashen Belarus da Iritiriya da Kirgistan da Bama da Sudan da kuma Tanzaniya.