Amnesty International da Human Right Watch
August 1, 2016'Yan kungiyar Amnesty International ba su ne 'yan kungiyar Human Right Watch ba, kungiyoyi ne guda biyu daban-daban. kungiyar Amnesty Internsational ta kafu a yakin duniya na biyu a lokacin da Shugaba Hitler na Jamus ya yi kisan kare dangi na Yahudawa sama da miliyan shida, Sai aka kalli wannan lamari a matsayin cin zarafin dan Adam a duniya inda aka bukaci wasu abubuwa wadanda suke gaba da shirye-shirye na doka ko kuma na tsarin mulkin kasa da kasa.
To bayan wannan lokaci ne aka tsara wasu kudirori na kare 'yancin dan Adam wanda kasashen da ke a matsayin membobi na Majalisar Dinkin Duniya za su bi wadannan kudirorin. To kokarin kare kudirorin shi ne ya sa wasu mashahuran 'yan siyasa, da masana harkokin shari'a da ma siyasar kasa da kasa, suka hadu suka kafa wannan kungiya ta Amnesty International.
Yadda aka kai ga kafuwar kungiyar Human Right Watch
To bayan tafiya ta yi tafiya ganin sai wasu suka lura cewa wannan kungiyar tamkar ta na nuna wasu abubuwa da suke da nasaba da banbanci, domin sai aka lura cewa bata cika sukar kasashe wadanda suke da alaka da Amerika ba, sai dai kananan kasashe kamar na Nahiyar Afirka, ko kuma Nahiyar Asiya, ko kuma Latin Amerika, ko kuma kasashen yankin Larabawa.
Wadannan korafe-korafe ne suka sanya wasu suka ja da baya tare da nuna dan yatsa ga Amnesty International. Saboda haka wasu kasashe, suka yi nazarin kafa kungiyar Human Right Watch wadda tafi mayar da hankali ga abubuwan da suka shafi ta'addanci, da ayyukan 'yan gudun hijira da matsalolin yake-yake, ko wata annoba daga Indallahi kamar ambaliyar ruwa. Amma kuma dukanninsu manufofinsu guda ne na kare hakkin dan Adam daga wani cin zarafi.