1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta koka kan cin zarafin 'yan jarida

Ahmed Salisu
November 2, 2018

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta koka kan yadda ta ce gwamnatin Sudan na cin zarfin 'yan jarida a kasar da ma yunkurin da ta ce ana yi wajen takaita aiyyukansu.

https://p.dw.com/p/37Xjg
Amnesty international
Hoto: picture-alliance/dpa/W.Kumm

Wani rahoto da Amnesty din ta fidda a wannan juma'ar ya nuna yadda gwamnatin Sudan din ta kame 'yan jarida yawansu ya kai sha biyar tsakanin watan Janairun wannan shekarar kawo yau. Wannan inji Sarah Jackson ta kungiyar ta Amnesty International wani yunkuri ne hana 'yan jarida yin aiki da kuma yin karen tsare ga damar da suke da ita ta fadin albarkacin bakinsu, wanda abu ne da bai kamata a ce an bari ya cigaba da wakana a kasar ta Sudan ba. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da a yau Majalisar Dinkin Duniya ke bikin ranar yaki da cinzgunawa 'yan jarida a duniya