1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurika ta jaddada goyan baya ga Isra'ila

August 1, 2012

Sakataran tsaron Amurika Panetta, ya gana da hukumomin Isra'ila inda ya bayyana yiwuwar kai wa Iran hari game da rikicin nukiliya

https://p.dw.com/p/15iAe
Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu, left, listens as U.S. Defense Secretary Leon Panetta speaks during a meeting at the Prime Minister's office in Jerusalem, Wednesday, Aug. 1, 2012. Israel's threats to attack Iran and the violence convulsing Syria top the agenda of Panetta's meetings Wednesday with Israeli government leaders. (Foto:Sebastian Scheiner, Pool/AP/dapd)
Panetta da NetanjahuHoto: dapd

Sakataran tsaron Amurika Leon Panetta, ya jaddadawa hukumomin Isra'ila goyan bayan fadar White House game da rikicin Iran.Panetta ya bayanan hakan a wata ziyara aiki da ya kai a birnin Tel -Aviv ,ya ce ko da mafaraki, Amurika ba za ta amincewa ba, Iran ta mallaki makaman nukiliya.

Saboda haka, za su cigaba da tuntuɓar juna da sauran ƙasashen duniya, domin cimma wannan buri.

Idan kuma aka kasa shawo kan lamarin ta fannin tattanawa,Panetta ya ce Amurika a shirye take ta yi amfani da ƙarfin soja.

" Kamin mu kai ga matakin amfani da tsinin bindiga sai mu haƙiƙance cewar tattanawa ta ci tura".

A yayin da yake nasa jawabi, ministan tsaron Isra'ila Ehud Barack, ya hurta cewa shi kam, ya yi imani da hukumomin Tehran ba za su amincewa ba su bada kai bori ya hau game da wannan batu, saboda haka maimakon a tsaya dogon turanci ,kamata tayi kawai a ɗaukan masu matakan ƙwaƙwara. Ya ce Isra'ila a shirye take ta fuskanci Iran ta fannin yaƙi idan hakan ta kama.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal