Amurka ta dakatar da bai wa Isra'ila tallafin makamai
May 8, 2024Amurka ta dakatar da bai wa Isra'ila tarin makamai da suka hada da bama-bamai, sakamakon fargabar far wa birnin Rafah da ke Kudancin Gaza da Amurkan ta yi, a karon farko kenan da shugaba Joe Biden ya janye tallafin tsaro ga Isra'ila.
Karin bayani:Biden ya caccaki Isra'ila kan salon yakinta a Gaza
Matakin na White House ya zo ne a makon da ya gabata, lokacin da Isra'ilan ta gaza yin cikakken bayanin da zai gamsar da Amurka kan batun, in ji wani babban jami'in Amurka.
Karin bayani:Shugaba Joe Biden na Amurka da Donald Trump sun caccaki juna a yakin neman zabe
Shugaba Joe Biden na fuskantar matsin lamba ta cikin gida, inda dubban daliban jami'o'in Amurka ke ci gaba da zanga-zangar adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, inda suke ci gaba da yin arangama da 'yan sanda.
A gefe guda kuma Mr Biden na fuskantar karin matsin lamba daga tsohon shugaban kasar Donald Trump, a daidai lokacin babban zaben kasar na watan Nuwamba ke karatowa.