Amurka ta dora wa jagororin Sudan takunkumai
June 2, 2023Talla
Sakataren harkokin wajen Amurkar Anthony Blinken ya sanar da cewa matakin kakaba takunkuman wani kashedi ne kan aika-aikar da sojojin Sudan da ma mayakan rundunar kar ta kwana na RSF ke aikatawa da ke kuntata wa rayuwar 'yan Sudan da ma dimukuradiyya.
Daga cikin abin da takunkuman suka kunsa, har da hana duk wani wanda ke da hannu a rikicin Sudan din izinin shiga Amurka da ma wasu wadanda za su durkusar da harkokin tattalin arziki.
Cikin watan jiya ne dai wakilan bangarorin da ke rikici a Sudan suka yi zama a Saudiyya inda suka amince da tsagaita wuta tare da kare fararen hula, amma kuma daga bisani aka ci gaba da kai wa juna hare-hare.
Amurkar dai ta ce a shirye take ta tsara tare da gabatar da wasu karin matakai a kan jagororin na Sudan.