Amurka ta kakkabo jirginta bisa kuskure a Tekun Bahar Maliya
December 22, 2024Sojojin ruwan Amurka guda biyu sun ketare rijiya da da baya, bayan da wani makami mai linzami da takwarorinsu suka harba bisa kuskure ya yi kaca-kaca da jingin da suke ciki a Tekun Bahar Maliya.
A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Amurka ta yankin Gabas ta Tsakiya ta ce direbobin jingin su biyu sun tsira da ransu sai dai guda daga cikin su ya samu raunuka ba masu muni ba.
Sanarwar ta kuma kara da cewa lamarin ya faru ne bisa kuskure ba wai don fuskantar matsin lamba daga abokan fada ba, kana kuma tuni an fara gudanar da bincike.
Karin bayani: Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen
A cewar rundunar tsaro ta Centcom, makamin mai linzami sunfurin USS Gettysburg ya kubce ne daga jirgin ruwan yakin Amurka USS Harry S.Truman kafin daga bisani ya cimma jirgin yakin sunfurin F/A-18 wanda ke dauke da matuka biyu.
Wannan lamarin na zuwa a daidai lokaci da Amurka ta shigar da ba wuya da 'yan tawayen Houthis na Yemen, wadanda ta ke kokarin fatataka.