An amince da yarjejeniyar kare muhalli
December 16, 2018Talla
Wakilan kasashen duniya a taro kan sauyin yanayi, sun amince da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Paris a shekara ta 2015. Taron wanda aka shafe makonni biyu ana yi tare da wakilcin kasashe kimanin 200 ya amince da batun kare yanayin na duniya ne da yammacin ranar Asabar.
A ranar Juma'a ce dai aka tsara kammala shi, sai dai gaza cimma matsaya kan yarjejeniyar ta birnin Paris ta tilasta kai shiga yammacin na Asabar. Daya daga cikin batutuwan da suka haifar da tarnaki a taron da aka yi a birnin Kotawice na kudancin Poland dai shi ne ko kasashe za su shigar da wasu karin manufofi a wa'adin da kuma iyakance wa kowace kasa ta cimma kafin shekara ta 2020. Akwai ma batun cinikin hayakin masana'antu a tsakanin kasashen.