An amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
May 10, 2014Talla
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar sun saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, cikin wani matakin martani daga matsin lambar kasashen duniya.
A wannan Jumma'a da ta gabata aka amince da yarjejeniyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan ya zama karo na farko da shugabannin suka fuskanci juna tun bayan barkewar rikici a watan Disamban 2013 kan gwagwarmayar samun madafun iko. Kiir da Machar sun amince da gwamnatin wucin gadi zuwa lokacin zaben shekara mai zuwa.
Bisa yarjejeniyar za a tsagaita wuta cikin sa'o'i 24.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal