SiyasaAfirka
Zaman makoki na kwanaki 3 a Nijar
October 3, 2023Talla
Sanarwar ma'aikatar tsaron kasar na cewar 'yan bindiga sama da 100 sun yi amfani da motoci da ke shage da bama-bamai wajen illata sojoji.
Sai dai ta yi ikirarin murkushe barazanar da 'yan ta'addan ke yi a wannan yankin da ya jima yana fama da hare-hare.
Harin da ke zama mafi muni ga sojojin tun bayan da suka hambarar da gwamnatin farar hula a watan Yulin da ya gabata, na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta amince da tayin shiga tsakani daga Aljeriya domin warware rikicin siyasa.
Tun a shekarar 2021 ne iyakokin kasashen Nijar da Mali da Burkina faso ke fama da ayyuukan yan ta'adda da ke da alaka da kungiyoyin al-Qaida da kuma na IS.