An bukaci a zauna lafiya a Kenya
September 22, 2017Talla
Babban Antoni Janaral na kasar ta Kenya Guthi Muigaia ya sanar da wannan mataki a wannan Juma'ar a yayin taron manema labarai, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma ke zaman dar-dar gudun abinda ka iya biyo baya bayan sanarwar dage zaben da hukumar zaben kasar ta fitar a jiya Alhamis, hukumar ta ce an dage zaben ne biyo bayan bayanai mai dauke da sarkakiya da kotun kolin kasar ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata hakan na nufi za a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 26 ga watan Oktoba.