Shugaban Rasha na shan suka kan Navalny
September 3, 2020Talla
Birtaniya ta bukaci Rasha ta fito fili ta bayyana gaskiyar lamarin, a yayin da ita kuma kungiyar EU ta yi wa batun kakkausar suka, daidai lokacin da a na ta bangare fadar gwamnatin Amirka White House ta bayyana cewa ta kadu da jin labarin, a yayin da Jamus ke shirin tattaunawa da kawayenta kan batun don cimma matsaya guda.
Binciken da aka gudanar a wani dakin gwaji na asibitin soja da ke Jamus, yayi nuni da cewa jagoran adawar na Rasha Navalny ya shaki wata guba ce mai sarke jijiyoyi, zargin da fadar gwamnatin Kremlin ta bayyana cewa za ta bayar da cikakken hadin kai wajen ci gaba da bincike, idan ta samu sakamakon farko na binciken da kwararru a fannin lafiyar suka yi a Jamus.