An ceto bakin haure a Sudan
September 12, 2018Talla
'Yan sandan kasar wadanda su ne suka tabbatar da wannan labarin, sun ce yayin wani sintiri na musamman da suka gudanar, sun kamo mutum 95, cikinsu kananan yara 85 daga hannun wasu bata-garin a Khartoum babban birnin kasar.
Ita ma rundunar 'yan sanda ta kasa-da-kasa wato Interpol, ta ce daga cikin yaran akwai wadanda aka tilasta wa shiga aikin hakar zinari a Sudan din.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa wadanda aka kaman na kokari ne na zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.
Mutanen dai sun fito ne daga kasashen Chadi da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Irititriya da Nijar da kuma Sudan ta Kudu.