1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Interpol ta ceto mutum 100 daga masu fataucin mutum

Ramatu Garba Baba
September 10, 2018

Hukumar 'yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta ce samamem hadin gwiwa da ta kai da 'yan sanda a wasu sassan birnin Khartoum na kasar Sudan, sun yi nasarar kubutar da mutane 100 daga masu fataucin dan adam.

https://p.dw.com/p/34ce6
Migranten aus Westafrika Symbolbild Menschenhandel
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Interpol ta ce jami'an sun yi nasarar cafke wasu mutane goma sha hudu wadanda ake zarginsu da laifin fataucin mutum a yayin samamen, hakazalika an same su da kudi kusan dala dubu ashirin. An gano yadda gungun ke yin garkuwa da 'yan cirani suna kuma neman kudin fansa.

An shirya tuhumarsu da laifukan safara da saka mutane aikin tilas da ma ci da gumin yara. Wadanda aka kubutar, sun fito ne daga kasashen Chadi da Jamhuriyar Demokradiyar Kwango da Iritiriya da kuma Nijar.