An ceto ma'aikatan jami'ar Abuja
November 5, 2021Talla
A ranar Talatar da ta gabata ce wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ma'aikatan jami'ar 4 da yaransu 2. Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Abuja Josephine Ader Anipr ta ce wadanda aka ceto sun sake ganawa da iyalansu.
A shekarun baya-bayan nan mussaman a arewacin Najeriya 'yan bindiga na garkuwa da gomman dalibai a makarantu don neman kudin fansa tare da kaddamar da munanan hare-hare a kauyuka.
Ci gaba da samun matsalolin tsaro a Arewa maso yammacin kasar da ma matsalar Boko Haram na tsawon shekaru 12 a Arewa maso gabashin kasar na jefa shakku kan makomar tsaron kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka.