1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto mutane 70 daga hannun IS a Iraki

Gazali Abdou tasawaOctober 22, 2015

Kawancen sojin Amirka da na Iraki da mayakan Kurdawa sun yi nasarar ceto mutane 70 da Kungiyar IS ta yi garkuwa da su a wani sansaninta da ke a Iraki.

https://p.dw.com/p/1Gssz
Befreite Gefangene aus dem Bagram Gefängnis in Afghanistan
Hoto: DW/Qadir Wafa

Ma'aikatan tsaron Amirka ta Pentagon ta bada sanarwar ceto mutane 70 daga ciki har da sojojin Iraki 20 wadanda kungiyar IS ta yi garkuwa da su a kasar Iraki. Ma'aikatar ta Pentagone ta ce an kuma kama mayakan Kungiyar ta IS biyar a cikin sumamen da kawancen sojojin Amirka da na Iraki da kuma mayakan kurdawan Irakin ya kai a wani sansanin mayakan Kungiyar ta IS .

Ma'aikatar tsaron Amirkar ta ce an kaddamar da sumamen kwato wadannan mutane ne bayan da suka samu bayanan da ke cewa Kungiyar ta IS na shirin aiwatar da kisan kan mutanen da suka yi garkuwa da su. An dai yi amfani da jiragen yaki masu dirar angulu wajen kai wannan hari wanda ya bada damar kama wasu takardun bayanan sirri na Kungiyar ta IS.

Sojin Amirka daya ya mutu a sakamakon raunin da ya ji a cikin masayar wutar da ta hada sojojin da mayakan Kungiyar ta IS.