An cimma matsaya da 'yan adawa a Kwango
December 23, 2016Wani kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa fararen hula kimanin 40 suka hallaka sakamakon rikici siyasa na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango, yayin da wasu kusan 500 suka jikata. An samu galibin tashe-tashen a Kinshasa babban birnin kasar gami da biranen Lubunbashi, da Boma gami da Matadi, inda ake zanga-zangar Shugaba Joseph Kabila ya ajiye madafun iko bayan karewar wa'adinsa na mulki.
Yanzu haka masu shiga tsakani suna fata bisa gani an warware rikicin kafin ya rincabe zuwa yakin basasa. Kuma tuni Firaminista Sami Badibanga na gwamnatin wucin gadi da aka nada ya yi alkawarin mutunta 'yancin dan Adam, kamar yadda yake cewa a majalisar dokoki:
Yanzu haka labarin da ke fitowa daga kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango na cewa bangarorin gwamnati da 'yan adawa sun cimma matsaya bisa manufa Shugaba Joseph Kabila ya ci gaba da rike madafun iko zuwa karshen shekara mai zuwa ta 2017. Kuma karkashin yarjejeniyar shugaban ba yi da ikon sake neman mulki a wa'adi na uku. Babban abin da ya rage shi ne idan bangarori suka amince da aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin Kiristoci mabiya darikar Katolika suka taimaka aka kulla.