An cimma yarjejeniyar rage dumamar yanayi a taron muhalli na Montreal
December 10, 2005Talla
An kammala babban taron kasa da kasa game da muhalli a birnin Monreal na Kanada tare da cimma yarjejeniyar daukar matakan rage dumamar doron kasa. Ministocin kare muhalli da suka halarci gun taron sun amince da ci-gaba da tattaunawa da nufin daukar karin matakan kare muhalli. Da farko dai kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Kyoto sun amince su tattauna dangane da kara wa´adin yarjejeniyar har bayan shekara ta 2012. A karkashin yarjejeniyar ta Kyoto kasashe kimanin arba´in masu karfin tattalin arziki sun dauki alkawarin rage yawan iskar dake gurbata yanayi da masana´antun su ke fitarwa kafin shekara ta 2012. To amma Amirka na adawa da yarjejeniyar.