1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fafatawa da ´yan tawayen Taliban a Afghanistan

June 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuK2

An kashe ´yan tawayen kungiyar Taliban su 6 a lokacin da suke kokarin yin garkuwa da wani dan sanda a lardin Paktia dake kudu maso gabashin Afghanistan. Ma´aikatar cikin gida ta ce sojoji da ´yan sanda sun yi mayar da martani akan ´yan tawayen bayan sun kai hari kan gidan jami´in dan sandan a ranar alhamis da daddare. A kuma canw ani yanki mai nisdan kilomita 100 gabas da Kabul babban birnin Afghanistan an kashe wani sojin kungiyar tsaro NATO a wani harin bam da aka kai kan motar dakarun kasa da kasa.