Yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu ta fara aiki
January 8, 2016Talla
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya ba da hakuri kan shekaru biyu da aka kwashe ana yakin basasa da babu kan gado. Kiir ya bayyana haka lokacin da yake bayyana sunayen 'yan majalisa 50 daga bangaren 'yan tawaye gami da amincewa da kafa majalisar ministoci da ta kunshi 'yan tawayen.
Tsohon shugaban kasar Botswana Festus Mogae ke shugabancin hukumar kula da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, inda aka amince da ministoci 16 daga bangaren gwamnati yayin da 10 za su fito daga bangaren 'yan tawaye.
Cikin watan Disamba na shekara ta 2013 yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati.