An fara jigilar yan gudun hijira na Angola daga Kongo
December 19, 2006Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD ta fara jigilar wasu daga cikinyan gudun hijira na Angola 1,800 wadanda suke zaune a JDK sheakaru da dama.
Wata sanarwa daga ofishin hukumar ta baiyana cewa kimanin yan gudun hijira 50 aka kwashe su jiya daga birni9n Kinshasa zuwa kudancin Angola.
Sanarawar tace nan zuwa karshen wata zaa ci gaba da jigilar yan gudun hijirar sau uku inda zaa rika kwasar yan gudun hijira 150 a kowace rana.
Yan gudun hijira ta Angola sun tserewa yakin basasa ne a kudancin kasar tun 1975 har zuwa 2002,ammam hukumar kula da yan gudun hijira tace nan zuwa karshen shekara zata mayarda 52,000 gida.
An kiyasta cewa yan kasar angola 145,000 ,cikin yan gudun hijira 224,000 daga kasashe makwabta da suke zaune JDK,hakazalika kuma yan gudun hijira na JDK kusan 410 ,000 kuma suke zaune a kasashe kamar su tanzania,Zambia da Kongo.