Kayan agaji sun fara isa yankin Jonglei
February 17, 2016A karon farko tun bayan barkewar rikici a Sudan ta Kudu a watan Disamban 2013, ayarin motocin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, sun samu sukunin kai kayan abinci a wasu yankunan jihar Jonglei a Sudan ta Kudu. Hukumomin agaji na kasa da kasa na fuskantar matsalolin kai agaji ga yankunan da ke fama da mastalar karancin abinci sabili da yakin basasan na Sudan ta Kudu. Binciken baya bayan nan ya nuna cewa kasar na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa, lamarin kuma da ya shafi mutane kimanin miliyan 2.8 wato kwatankwacin kashi 25 cikin 100 na al'ummar kasar baki daya, inji Joyce Luma daraktar hukumar WFP a Sudan ta Kudu:
"A bana bazara za ta fara da wuri saboda haka za a samu karin yawan mutane da za su fuskanci matsananciyar yunwa a tsukin wannan lokaci."