1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kame bayan gobara a wani gidan rawa a Brazil

January 28, 2013

Yayin da aka fara gudanar da jana'izar wadanda suka mutu a wata gobara a wani gidan rawa a Brazil, 'yan sanda sun kame wasu mutane da ake zargi da hannu a gobarar.

https://p.dw.com/p/17T8s
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan sanda a Brazil sun kame mutane uku bayan gobarar nan da ta tashi a wani gidan rawa dake birnin Santa Maria a karshen mako. Kamar yadda kafofin yada labaru suka nunar daga cikin mutanen dake hannun hukumomin har da mai gidan rawar da kuma biyu daga cikin mawakan da a lokacin da suke wasa gobarar ta tashi, wadda kuma ta halaka akalla mutane 230. Bisa bayanan da likitoci suka bayar akasarin wadanda suka mutum sun shaki hayaki ne ko kuma an tattake su lokacin turmutsitsi. A halin da ake ciki an fara gudanar da jana'izar wadanda bala'in ya rutsa da su. Wani da ya halarci jana'izar cewa ya yi: "Na ga ana binne 'yan'uwa juna biyu, dan'uwa na binne na dan'uwansa, yanzu yanzu kuma an gaya mini cewa daya daga cikin abokanne na ya mutu."

Shugabar Brazil Dilma Rousseff ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasa baki daya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi