An fara kwashe mutane daga yankunan Mexico, da Cuba da kuma Florida saboda kwararowar guguwar iskar nan Wilma.
October 20, 2005Jami’an ceto a kasashen Mexico da Cuba da kuma na jihar Florida a kasar Amirka, sun fara daukan matakan kwashe jama’a daga wasu yankunan kasashensu, wadanda guguwar iskar nan Wilma ke barazanar afka musu. Hukumomin nazarin canje-canjen halayen yanayi sun ce tuni dai, guguwar, mai saurin kilomita dari 2 da 70 a ko wace awa daya, ta janyo ambaliyar ruwan sama a wasu yankunan. Kuma a halin yanzu, ta nufi jihohhin tsakiyar Amirka. Wasu rahotanni sun ce, a kasar Haiti, guguwar ta janyo asarar rayukan mutane 11. Mahukuntan kasashen Honduras da Nicaragua su ma sun fara daukan matakan kwashe jama’a daga wasu yankunan da ake zaton guguwar za ta iya afka wa.
Wannan guguwar, wadda aka yi wa lakabin Wilma, ita ce ta 12 a wannan shekarar, da ta addabi yankunan Carribean da kuma tsakiya da kudancin Amirka.