An samu rigakafin cutar maleriya
October 6, 2021Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da fara amfani da rigakafin cutar zazzabin cizon saura na Maleriya ga yara a nahiyar Afirka, abin da ke nuna fata kan magance wannan cuta da take addabar mutane a kasashe masu zafi.
Bayan taro da masu ba da shawara ga hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, shugaban hukumar ta lafiya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce wannan lokaci ne na tarihi. A shekara ta 2019 cutar zazzabin cizon saura na maleriya ta halaka fiye da mutane dubu-380 a nahiyar Afirka, inda ake kashi 94 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a nahiyar mai mutane milyan-dubu da milyan 300. Galibin wadanda cutar ke kashewa yara ne 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.
Samar da rigakafin cutar zazzabin cizon saura ya zama gagarumin abin da yake da tasiri a nahiyar Afirka.