An fara rigakafin Ebola a Kwango
August 2, 2019Talla
Masu binciken lafiya a Yuganda sun kaddamar da aikin rigakafin cutar nan ta Ebola a makwabciyar kasar wato Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango inda annobar ta halaka sama da mutum dubu da 800.
Rahotanni sun ce an yi nasarar yi wa yara 'yan makarantun firamare da na Sakandare 240 cikin 300 da ke yankin Goma da abin ya yi zafi.
Ana kuma sa ran mutum 800 ne za a yi wa rigakafin maganin da kamfanin Janssen Pharmaceuticals ke yi tare da tallafin kungiyar likitoci masu bada agaji ta Borders.
Tun da fari dai an sanar da samun mutum na hudu da ya kamu da cutar a gabashin birnin Goma, yankin da ke dauke da mutane kimanin miliyan biyu.