An fara samun sakamakon farko na zaben kasar Tanzaniya
October 26, 2015Talla
Masu zabe na kasar Tanzaniya na ci gaba da jiran sakamakon zaben wannan Lahadi da aka yi fafatawa mai zafi tsakanin John Magufuli na jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi mai mulki da kuma Edward Lowassa tsohon firaminista da ke bangaren adawa. Sakamakon farko na wuraren da aka samu ya nuna jam'iyya mai mulki ke kan gaba.
A tsirin Zanzibar mai kwarya-kwaryar 'yanci tuni dan takara na jam'iyyar adawa Seif Sharif Hamad ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe gabanin sakamakon na hukuma. Hamad mataimakin shugaban yankin a gwamnatin hadaka.
Yanzu haka babban jam'iyyar adawa ta kasar Tanzaniya ta bayyana cewa mahukuntan sun cafke mata masu aikin sa-kai na zabe mutane 40, lokacin zaben na kasa baki daya.