An fara samun tashin farashin mai a duniya
December 1, 2016A karon farko cikin shekaru takwas kungiyar kasashe masu arzikin man fetir wato OPEC ta dauki matakin rage yawan danyen mai da take hakowa, matakin kuma da janyo tashin farashin danyan mai tun daga wannan Laraba. Yanzu haka dai farashin gangar man ta haura dalar Amirka 50. A gun wani taron membobin kungiyar da ya gudana a birnin Vienna na kasar Austriya kungiyar ta OPEC ta amince da wasu matakai da nufin rage yawan mai da suke sayarwa a duniya don bunkasa farashinsa. Masharhanta da dama sun yi tsammanin kungiyar za ta gaza amincewa da yarjejeniyar rage yawan man saboda rarrabuwar kai tsakanin manyan kasashen OPEC din wato irinsu Iran da Saudiyya gabanin taron. Farashin gangar man dai ya tashi da fiye da kashi 10 cikin 100 jim kadan bayan cimma yarjejeniya ta OPEC.